Rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ta cafke wasu jami’anta 5 da laifin bindige wani yaro dan shekara 17 da haihuwa mai suna Ibuchim Ofezie a garin Jos.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya bayyana cewa za a hukunta jami’an da abin ya shafa bayan gudanar da cikakken bincike.
“An tattaro cewa, a wani yunkuri na tabbatar da dokar hana zirga-zirgar babura a jihar, jami’an sun ziyarci kasuwar tasha tare da fatattakar wadanda ke gudanar da ayyukan ba bisa ka’ida ba. Ana cikin haka sai suka yi ta harbe-harbe, harsashin da ya bata ya afkawa Ofezie a cikin shagonsa dake kasuwa.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Filato, CP Bartholomew Onyeka, ya yi Allah wadai da kisan wani matashi dan shekara 17, Ibuchim Ofezie, mazaunin unguwar Agingi da ke karamar hukumar Bassa a garin Jos da wasu ‘yan sintiri da ke aiki a sashin “C” suka yi.