fidelitybank

An cafke ‘ya’yan jarumin Nollywood bayan sun sace masa Naira miliyan 55

Date:

Rundunar ‘yan sanda ta kama ɗa da kuma ɗiyar fitaccen jarumin fina-finan barkwancin nan na Najeriya, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, bisa zargin satar gudunmawar kuɗin da aka shirya domin jinyar jarumin.

Ana zargin Onyeabuchi Okafo da Jasmine Okekeagwu da laifin “daukar wayar jarumin tare da yin kutse cikin bayanan bankinsa”, kafin suka sace naira miliyan 55.

Kuɗaɗen dai na daga cikin gudunmawar kuɗaɗen da masoyan jarumin suka bayar domin jinyarsa, bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya a bara.

Cutar ta yi sanadin yanke kafar Okafor daya. An kuma yi wa tauraron nollywood din tiyata biyar, in ji iyalansa.

Hukumomin ƙasar dai sun ƙwato naira miliyan 50, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Mayegun Aminat ya bayyana.

Ƴaran nasa da ake zargin na shirin tserewa ne zuwa Birtaniya, a cewar Aminat.

Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun kuma ruwaito cewa wata kotu a Legas ta saki mutanen biyu kan belin Naira miliyan 15 yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Ana sa ran za su gurfana a gaban kotu a watan Maris don ci gaba da sauraren karar.

vgn news 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp