Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama ƴan shi’a 97 domin gurfanar da su gaban kotu, bayan wani rikici da ya barke tsakaninsu da ƴansanda a kasuwar Wuse da ke Abuja ranar Lahadi.
Rikicin da mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda biyu, yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka, da kuma lalata motocin ‘yan sanda guda uku da kungiyar ta Shi’ar ta yi.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansanda, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Litinin ya bayyana cewa sahihan bayanan sirrin da suka samu ne ya bai wa jami’an ‘yan sanda damar kame wadanda ake zargin.
Ya kuma jaddada cewa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin a tsaurara matakan tsaro a kan lamarin.
Sufeto-Janar ɗin ya nanata kudurin ‘yan sanda na kame duk wadanda ke da hannu a rikicin tare da tabbatar da sun fuskanci shari’a.
Ya kuma sha alwashin hana duk wani nau’i na tarzoma a faɗin ƙasar, yana mai jaddada aniyar rundunar na tabbatar da doka da oda a fadin kasar.
Egbetokun ya yi Allah wadai da kisan gillar da ƴan shi’an suka yi wa jami’an ‘yan sandan, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin yarda.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, ‘yan sanda sun ƙuduri aniyar bankaɗo cikakken bayanin harin da kuma hana cin zarafin jami’an tsaro.