fidelitybank

An cafke wasu da ake zargi da sace-sace a Jos

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin barayin mota ne a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mista Alfred Alabo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba a Jos.

Alabo ya ce an gano wata motar Ford Explorer mai lamba SHD 452 JT da chassis mai lamba 1FM5K8D81EGB13576 da aka ce an sace a Aja da ke jihar Legas a karamar hukumar Langtang ta Kudu da ke Filato.

“Tare da dabarun yaki da satar motoci da kwamishinan mu, Mista Steve Yabanet ya amince da shi, a kwanan baya rundunar ta kwato wata mota da aka sace tare da cafke mutane biyu da ake zargi.

“Wadanda ake zargin, Godiya Amos mai shekaru 33 da kuma Polycarp Abu mai shekaru 38, za a gurfanar da su gaban kotu bayan bincike.

“A yanzu haka motar tana hannunmu kuma nan ba da jimawa ba za a mika ta ga rundunar jihar Legas da zarar an kammala bincike,” inji shi.

A cewarsa, kwamishinan ya gargadi dukkan masu aikata laifuka a Filato da su daina aikata laifuka, ya kara da cewa rundunar za ta biyo bayansu.

sun news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp