A wani gagarumin samame da suka kai, dakarun runduna ta 6 da Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kama ɗan ta’addan da ake zargi da kitsa harin da aka kai a ƙauyen Mararaban Azagawa da ke ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba.
Rundunar ta ce kamen ya biyo bayan harin da aka kai ranar 16 ga watan Yunin 2024, wanda ya yi sanadin asarar rayuka biyar da jikkata mutane da dama.
Muƙaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
A cewarsa, dakarun da ke sansanin ‘Forward Operating Base’ a ƙaramar hukumar Bali, sun ƙaddamar da wani samame na musamman bayan sahihan bayanan sirri da suka samu domin kamo waɗanda suka kai harin.
A yayin samamen ne sojojin suka kama wanda ake zargin shi ne ya kitsa harin mai suna Hassan Ibrahim wanda aka fi sani da Godu, ɗan shekara 39, kamar dai yadda sanarwar ta ce.
A yayin da ake kamen, sojojin sun ƙwato manyan makamai da harsasai, da kuma babur na ɗaya daga cikin waɗanda harin ya shafa.
Rundunar sojin ta ce wanda ake zargi ya amince cewa yana da hannu a harin kuma yana bayar da bayanai masu mahimmanci da za su kai ga kama sauran waɗanda ke da hannu a ciki.
A halin da ake ciki, kwamandan rundunar 6 Brigade Sector 3 OPWS, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa jama’a bisa bayar da bayanai masu amfani da suka kai ga kama waɗannan mutane.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da mara wa jami’an tsaro wajen aikin kawar da masu aikata laifuka a jihar Taraba.