Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa masu aikata laifuka makamai a jihohin Kano da Jigawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Wadanda ake zargin da suka hada da Bilal Faraji mai shekaru 29 da Yusuf A. Yusuf mai shekaru 28, an kama su ne a lokacin da suke ba da bindigogi ga masu aikata laifuka a kan hanyar Ringim.
A cewarsa, “A ranar 03/10/2023 da misalin karfe 0900 na safe an kama Bilal Faraji na jamhuriyar Nijar da Yusuf A. Yusuf na karamar hukumar Kazaure jihar Jigawa dauke da bindigu da alburusai wadanda suke kaiwa ga wasu marasa kishin kasa dake addabar garin Ringim da kewaye. .’
Ya ce da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa laifin sayar da bindigogi a cikin jihohin Kano da Jigawa.
Shiisu ya ce ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu domin gurfanar da su gaban kuliya.