An kama tsohon kwamandan sojin Bolivia saboda abin da gwamnati ta bayyana a matsayin yunkurin kifar da gwamnati.
An tsare Janar Juan Jose Zuniga bayan da ya girke daruruwan sojoji da motocin yaki a tsakiyar birnin La Paz.
Ya bukaci a sauya gwamnati. Shugaba Luis Arce ya nada sabbin kwamandojin soji.
Wani sanata daga bangaren hamayya, Andrea Barrientos ya zargi shugaban kasar da hannu a kitsa kifar da gwamnatinsa a kokarin da yake na samun goyon baya a gida da kuma sauran kasashen duniya.
An kori Janar Zuniya a ranar Talata bayan ya fada wa wani gidan Talabijin cewa zai yi duk mai yiwuwa don dakile tsohon shugaban kasar Evo Morales daga komawa kan mulki. In ji BBC.