‘Yan sanda sun cafke wani mutum da ya yi yunkurin cinnawa wani masallaci wuta a birnin Dresden na Jamus da yammacin jiya Talata.
Mutumin ya zubar da fetur a gaban wani masallaci kuma ya yi kokarin cinnawa ginin wuta, in ji kakakin ‘yan sandan.
Shaidu sun kira lambar hukumar bayar da agajin gaggawa bayan da suka ga mutumin yana zube man fetur a wajen masallacin, wanda a lokacin ya cika.
An kama mutumin mai shekaru 34, kuma yana karkashin binciken ‘yan sanda kan yunkurin tada kayar baya.
Duk da cewa da farko ba a san dalilinsa ba, an ce wanda ake zargin ya kona kwafin Alkur’ani mai girma a wani masallaci a watan Afrilu.