‘Yan sandan ƙasar Sifaniya sun ce, sun kama wani mutum da ake zargi da cin zarafin wata ‘yar jarida bayan da aka ce ya taɓa ta a lokacin da take ba da rahoto kai tsaye a gidan talabijin.
Isa Balado dai tana ba da rahoto kan fashin da aka yi a Madrid a ranar Talata inda aka ce mutumin ya shigo ya taɓa mazaunanta, wanda ya musanta hakan lokacin da ta fuskanci shi.
Balado ta yi ƙoƙarin ci gaba da aikin ta, amma mai gabatar da shirin ya katse ta.
“Isa, ki yi haƙuri na katse ki, amma mutumin nan taɓa ki ya yi?” Nacho Abad mai gabatar da shirin ya tambaye ta.
Da ƴar jaridar ta tabbatar da hakan ne ya faru sai Abad ya umurce ta da ta ɗauki mutumin a kyamara.
An dai nuna mutumin tsaye da Balado a kyamarar yana ta murmushi da raha yayin da ya musanta zargin.
Daga baya dai ‘yan sandan sun ce an kama mutumin da laifin cin zarafin ‘yar jarida a wani saƙo da suka wallafa a shafin su na X.


