Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce, ta kama wani mutum da ake zargin ya kashe dan sa tare da kona gawarsa a kauyen Ebe Ikpe da ke karamar hukumar Essien Udim a jihar.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Odiko Macdon, wanda ya zanta da manema labarai a ranar Talata, hakimin kauyen, Cif Akpan Aniekan, da shugaban karamar hukumar, Sylvester Akpan ne suka kai rahoton faruwar lamarin a hedikwatar ‘yan sanda ta Essien Udim. .
SP Macdon ya shaida wa manema labarai cewa: “Sun ruwaito cewa wani Innocent Uko na Ebe Ikpe ya yi amfani da adda wajen kashe dansa, Boniface Innocent Uko, mai shekaru 26, ya kona gawar sa, sannan ya jefar da gawarwakin a wani bayan gida da aka yi watsi da shi a cikin gidansa don boye lamarin.
“A bisa karfin rahoton, jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wurin [sun gano] gawar da ta kone, yanzu an ajiye a dakin ajiye gawa. An kama wanda ake zargin, kuma ya amsa laifin kashe marigayin, bisa dalilan rashin da’a da cin zarafi da abin kunya.”
Kakakin ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa rundunar ta kama Charley Edem John, wanda ake zargi da satar kananan yara biyu ‘yan shekara bakwai.
“Rundunar, bisa wani rahoto na sirri, ta kama Charley Edem John, wanda ya sace yara biyu, kowace shekara bakwai, daga makarantarsu. Wanda ake zargin ya yi amfani da dan uwansa, mai shekaru 10 kuma a makaranta daya, wajen fitar da yaran daga ajinsu,” in ji Macdon.
A cewar kakakin ‘yan sandan, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike a kan su.


