Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Habu Ibrahim dan shekara 40 bisa zarginsa da baiwa matarsa guba a kauyen Danadama da ke karamar hukumar Sule Tankarkar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, A T. Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne bisa zarginsa da lakada abin sha da nama da guba, inda ya nufi matarsa mai suna Zakiya Uzairu mai shekaru 35 da nufin ya gaji dukiyarta.
Ya ce da samun rahoton, jami’an tsaro na sashen Sule Tankarkar sun yi gaggawar kama wanda ake zargin a wurin.
CP. Abdullahi ya ce an kawo wanda ake zargin ofishin ‘yan sanda shiyya da ke Sule Tankarkar domin yi masa tambayoyi, daga bisani kuma aka mika shi zuwa sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) da ke Dutse don ci gaba da bincike.
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yarda da aikata laifin, inda ya tabbatar da sahihancin bayanan da aka baiwa ‘yan sanda.
“Ya amince da niyyar kashe matarsa domin ya mallaki dabbobinta, da suka hada da awaki, tumaki, da shanu.
“Ya ce matar da kyar ta tsere bayan ta gane gubar kuma ta yi tunanin shirinsa,” in ji ‘yan sandan.