‘Yan sandan Jamus sun cafke wani mutum da ake zargi da daba wa mutane wuka a daren juma’a a yammacin birnin Zolinhen. ‘Yan sandan sun ce mutumin mai shekara 26 da kan shi ya je ya mika kanshi a wajensu, tare da ikirarin shi ne ya aikata harin.
Mutane uku ne suka mutu wasu 8 suka jikkata a lokacin da aka kai harin ana tsaka da bikin cikar birnin Solingen shekara 650 da kafuwa.
Kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS ta dauki alhakin kai harin, koda yake ba a tabbatar da hakan ba.
To amma kuma mutumin da aka kama da laifin kai harin dan asalin Syria, wanda kum ake zarin yan da alaka da kungiyr ta IS.