Wasu mutum biyu na fuskantar tuhuma kan yunkurin kisan kai a Afirka ta Kudu bayan da wasu yara kusan 90 suka kamu da rashin lafiya bayan cin fanke da aka sanya wa tabar wiwi.
Jamiāai sun ce yaran sun sayi fanken ne a wajen wani mutum a gefen titi a kan hanyarsu ta zuwa makarantar firamare ta Pulamadibogo, a arewa maso yammacin Pretoria. In ji BBC.
An kai da dama daga cikinsu asibiti saboda tashin zuciya da ciwon ciki da kuma amai.
An zargi mutanen biyu masu shekaru 21 da kuma 19 da yunkurin aikata kisa a ranar Jumaāa.
Ma’aikatar ilimi ta lardin Gauteng ta ce malamai sun kira motar Éaukar marasa lafiya bayan da suka lura cewa Éalibansu sun fara nuna wasu halaye a cikin aji.
Ta ce lamarin ya haifar da damuwa matuka ga iyayen yaran.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar, ta ce an garzaya da dukkan Éaliban zuwa asibitoci da ke kusa, inda zuwa yanzu aka sallami kusan 87.
Ma’aikatar ta ce Ę“an mata uku ne kaÉai suka rage a asibiti, kuma suna ci gaba da samun kulawa yadda ya kamata.