fidelitybank

An cafke mutane uku da ake zargi da yin fashi da makami

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce, ta kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da kuma ‘yan kungiyar asiri mai suna Eiye a garin Benin, babban birnin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Chidi Nwabuzor ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.

A cewarsa, “’yan fashi da makami uku da kuma ‘yan kungiyar Eiye Secret Cult Confraternity sun shiga hannun jami’an rundunar yaki da fashi da makami na hedikwatar ‘yan sanda ta Ugbekun, Benin ranar Lahadi.”

Ya ce ‘yan sandan sun kai farmaki wani Otal da ke kan hanyar Enomayo, Off Upper Sakponba Road, Benin, inda suka kama wani Bright Omonowa Clifford Patrick, da Isaac Peter tare da kwato bindiga guda daya da aka kera a gida da kuma Black Beret na Eiye Secret Cult Confraternity.

Ya ce an kama su ne biyo bayan samun sahihan bayanan sirri kan taron sirri da wadanda ake zargin suka yi a otal din.

PPRO ta yi nuni da cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Dankwara, ya gargadi ‘yan kungiyar asiri daban-daban da masu daukar nauyinsu da su daina ayyukan da suke yi a jihar ko kuma su fuskanci fushin doka.

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp