Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta ce jami’anta sun ki karbar cin hancin Naira 800,000 tare da kama wasu mutane akalla uku dauke da nadi guda goma sha biyu na wayoyi na tagulla da ake zargin an sace su a sandar wutar lantarki.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da DSP Sanusi Abubakar, mai magana da yawun rundunar ya fitar a Sokoto ranar Alhamis.
Ya ce ‘yan sandan da ke sintiri a kan hanyar Birnin Kebbi a jihar sun tare wata motar kirar Volkswagen Sharan mai Reg. No. KSF 356 Lagos, makil da wayoyi.
“Wadanda ake zargin, Rufa’i Sani, Yusha’u Abubakar da Ahmadu Bello, sun yi yunkurin baiwa ‘yan sanda cin hancin Naira 800,000 domin su samu damar wucewa.
“Duk da haka, ‘yan sandan mu sun tattara kudaden a matsayin baje kolin kuma suka kawo wadanda ake zargin tare da motar su zuwa sashin binciken manyan laifuka da bincike na jihar don bincike mai zurfi,” in ji shi.
Kakakin ya kuma ce a ranar 13 ga watan Mayu, wata tawagar jami’an ‘yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na Bodinga a jihar a kan aikin ‘yan sandan gani da ido sun kama wasu mutane hudu da wayar tagulla.
“Da aka gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifin hada baki da wani Habibu Nimadi tare da lalata taransfoma.
“Amma binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa tiransfomar na nan a unguwar Kauran Mido a karamar hukumar Bodinga,” ya kara da cewa.
Abubakar ya kuma mika yabo ga kwamishinan ‘yan sanda, Ali Kaigama, ga mutumin da ya nuna kwazon kwarewa ta hanyar kin karbar cin hanci.
Ya ce hukumomin tsaro a jihar suna yin gargadi mai tsanani ga ’yan kasa marasa kishin kasa da ke lalata kayayyakin gwamnati don su daina aikata wannan aika-aika ko kuma su fuskanci illa.
Abubakar ya ce: “Rundunar ta kuma yi gargadi kan duk wani yunkuri na aikata duk wani abu da ba a so ba kafin, lokacin da kuma bayan kaddamar da shi mai zuwa.
“Rundunar ‘yan sanda tare da dukkan hukumomin tsaro, za su hada kai yadda ya kamata, wajen tunkarar duk wanda ya yi yunkurin kai hari kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, ba tare da wani dalili ba.
“Hukumar tana kuma tabbatar wa da jama’a cewa za ta ci gaba da aikin sintiri da kuma kai farmakin maboyar ‘yan ta’adda har sai mutanen jihar sun kwanta da idanunsu biyu.”