Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ta ce, tare da hadin gwiwar ‘yan uwa jami’an tsaro sun cafke mutane 30 da ake zargi da aikata laifuka a fadin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Damaturu.
A cewarsa, daga cikin wadanda aka kama akwai Mohammed Garba mai shekaru 25 da kuma Ibrahim Mohammed mai shekaru 22 bisa zargin kashe wani mutum da suka shiga gidansa da laifin sata.
“Rundunar ta na jajantawa iyalan mamacin tare da tabbatar wa al’umma hukuncin da ya dace kan masu laifin.
“Duk da haka, yawancin masu laifin da aka kama sun yi zaman gidan yari a baya daga irin wannan laifuka”, in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da: wuka da wayoyin hannu guda biyar na nau’ukan iri daban-daban.
“A halin da ake ciki, tun daga lokacin da aka fara gudanar da bincike na musamman don gurfanar da shi a gaban kotu domin hukumar ta bukaci nagartattun mutanen al’umma da su tallafa wa jami’an tsaro ta hanyar samar da bayanai masu amfani na duk wani yunkuri da ake zargi da kuma maboyar masu laifi,” in ji shi.