fidelitybank

An cafke mutane 3 da suka yi wa Vinicius wariyar launin fata a Laliga

Date:

Ƴan sanda a Sifaniya sun kama wasu mutane uku masu goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Valencia bisa zarginsu da cin zarafin dan kwallon kungiyar Real Madnid Vinicius Junior ta hanyar kalaman wariyar launin fata.

Daga cikin mutanen uku har da wani bakar fata, sanna kuma ƴan sandan sun sanar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da rataye mutum-mutumin Vinicius din.

Lamarin ya janyo ka-ce-na-ce a Brazil, sannan gwamnatin kasar ta bukaci ganawa ta musamman da ministocin Sifaniya da masu gabatar da kara da kuma hukumar kwallon kafar kasar.

A lokacin karawar Valencia da Real Madrid ne aka ci zarafin Vinicius, wanda karon farko kenan da aka ba shi jan kati a tarihin sana’arsa ta taka leda, ya fuskanci kalaman wariya da na cin zarafi karo da dama a La Liga a kakar nan.

An dan dakatar da karawar a zagaye na biyu, bayan da dan kwallon Real din ya nuna bacin ransa kan kalaman wariyar da ake rerawa.

Daga lokacin ne ransa ya baci har ta kai da aka ba shi jan kati a fafatawar da aka ci Real 1-0, karo na takwas da ta yi rashin nasara a La Liga a bana.

Ita kuwa Valencia, wadda ta ci wasan ta yi sama zuwa ta 13 da tazarar maki biyar tsakaninta da ‘yan ukun karshen teburin La Liga

nigerian 
newspapers today the sun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp