Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama mutane 18 da ake zargi ake zargi da kai hari ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kan titunan jihar nan.
Kwamishinan ‘yan sandan, Usaini Muhammad Gumel ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai da ya yi a ranar Litinin.
A cewarsa, an kama mutanen ne a wasu wuraren da aka gano a maboyar masu aikata laifuka a cikin birnin jihar nan.
Ya ce, rundunar ta samu nasarar kama su ne a yankunan Mazaunar Tanko da Dandishe da Kofar Dan Agundi da Kofar Mata da kuma Filin Idi.
Sauran sun hada da Kofar Na’Isa da Kwanar Diso da Kukar Bulukiya tare da Dorayi Babba.
Kwamishinan ya kuma ce, abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da muggan makamai da kuma tabar wiwi.
Gumel ya kara da cewa duk wadanda ake zargin za a tantance su yadda ya kamata, kuma bayan kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.