Jami’an ‘yan sanda a jihar Adamawa sun kama wasu matasa 15 na wata kungiya mai suna Shila Boys, wadanda suka kware wajen kwace wayoyi da sauran kayayyaki daga mazauna garin.
Rundunar ‘yan sandan jihar, wacce ta sanar da kamun na baya-bayan nan ta wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Suleiman Nguroje, ta ce an gano wayoyin hannu guda tara da injin POS da muggan makamai da kuma muggan kwayoyi.
Sanarwar ta ambaci sunayen wadanda ake zargin kamar haka: Abdullahi Shuaibu, 18; Auwal Saleh, 18; Usman Abdullahi, 21; Auwal Isah, 20; Usman Ahmadu, 32; Muhammad Abubakar, 18; da Jamilu Hassan, 19.
Sauran su ne Abdulsalam Abdullahi mai shekaru 20; Salisu Umar, 19; Yahaya Umaru, 25; Salahudeen Auwal,18; Yusuf Ahmed, mai shekaru 20; Jamilu Sani, 18; Abraham Joel, 18; da Muhammad Auwal, 19.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama wadanda ake zargin ne a daidai lokacin da aka kammala bikin Sallah a garin Yola da ke karamar hukumar Yola ta Kudu, da Jimeta a karamar hukumar Yola ta Arewa da kuma kewaye.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar, CP Dankombo Morris, ya yabawa mutanen jihar Adamawa bisa hadin kan da suke bayarwa wajen yaki da fashi da makami, fasa gidaje da kuma munanan laifuka na kungiyar asiri ta ‘Shila’,” in ji sanarwar ta ‘yan sandan.