Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta bayyana cewa, ta kama wasu matasa fiye da 100 bisa zargin su da shirya shagulgulan auren ‘yan luwaɗi da maɗigo a wani otal.
Rundunar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X (Twitter), kuma ta ce nan ba da daɗewa ba za ta gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan sanya hannu kan dokar hana luwaɗi da maɗigo a shekarar 2014, jami’an tsaro sun kama mutanen da ake kyautata zaton ‘yan luwadi ne tare da gurfanar da su gaban shari’a.
A watan Disambar 2020, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama mutum 10 da ake zargi da aikata luwadi a wani gidan karuwai.
A shekarar 2018 kuma, ‘yan sanda sun kama wasu maza 57 bisa zargin yin luwadi a otal.
Haka zalika ma a watan Janairun 2022, an kama wasu mutane takwas da ake zargi su ma da yin luwadi da wani otal.
Rahotanni dai sun ce dokar hana luwadi a shekarar 2014 ta tanadi daurin shekara 14, ga duk wanda aka samu da laifin yin jima’i da jinsi ɗaya.


