fidelitybank

An cafke Matsafa biyu da yunƙurin asirce shugaban ƙasa

Date:

Hukumomin Zambiya sun kama wasu mutum biyu da ake zargi ”matsafa” ne da aka bai wa aikin asirce shugaban ƙasar.

‘Yansanda sun ce sun kama Jasten Mabulesse Candunde da Leonard Phiri a Lusaka, babban birnin ƙasar.

“Aikin da suka ƙudiri aniyar yi shi ne amfani da layu wajen cutar da shugaba Hakainde Hichilema”, kamar yadda sanarwar ‘yansandan ta bayyana.

Mutane da dama a ƙasar da ke kudancin Afirka sun yi amanna da bokaye, inda a lokuta da dama mutane kan rayu da fargabar tsoron asiri.

‘Yansanda sun yi zargin cewa Nelson Banda – ƙanin wani ɗan majalisa Emmanuel Banda, da aka fi sani da “Jay Jay” Banda – ne ya bai wa bokayen aikin sabauta shugaban ƙasar.

A watan da ya gabata ne aka kama ɗan majalisar a makwabciyar ƙasar Zimbabwe kan zargin laifin fashi, zargin da ya musanta.

Sanarwar ‘yansanda ta ce wanda ake zargi da bai wa bokayen aikin ya tsere, inda suka alƙawarta farauto shi.

An dai kama bokayen ƙarƙashin dokokin tsafi na ƙasar, inda ake zarginsu da aikata tsafi da zaluntar dabbobin, bayan da ka same su da tarin guraye da layu da kuma hawainiya da ranta, kamar yadda ‘yansanda suka yi bayani. A cewar BBC.

Bokayen sun kuma bayyana wa ‘yansanda cewa an yi musu alƙawarin kuɗin ƙasar fiye da kwaca miliyan biyu kimanin dala 73,000, idan suka kammala aikin sabauta shugaban ƙasar.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp