Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama wani matashi mai suna Abubakar Haruna mai shekaru 27 da haihuwa da laifin satar igiyoyi a wata taransfoma a yankin Onikan na jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamun a wani sakon da ya rabawa manema labarai a shafin sa na X ranar Asabar.
Hundeyin ya ce jami’an ‘yan sanda sun kutsa kai wurin da lamarin ya faru ne bayan da aka yi masa waya inda suka kama wanda ake zargin.
“Bayan kiran da jami’an Dibishin Onikan suka kai musu ne suka kama wanda ake zargin bayan da ya tsallake rijiya da baya ya yanke igiyoyi daga na’urar taranfoma da ke cikin harabar.
“An kama shi da adduna, zato biyu da fila,” in ji mai yin hoton.
Kakakin ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.