fidelitybank

An cafke matashin da ake zargi da kashe Mahaifiyarsa da kanwarsa

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, ta cafke wani matashi da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa mai suna Misis Charity Orji da ‘yar uwarsa Miss Ukamaka Orji tare da binne su a wani kabari mara zurfi a cikin lambun su.

Wanda ake zargin, Somadina Orji dan kabilar Igboariam a jihar Anambra, an ce ya aikata laifin ne a ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023, a Umuagu Inyi da ke karamar hukumar Oji.

Bisa bayanai da dama da faifan bidiyo na faruwar lamarin, marigayiya Charity, wacce aka haifa a garin Inyi amma tayi aure a Igboariam, jihar Anambra, ta kasance a gidan danginta da ‘ya’yanta tsawon shekaru.

Rahoton ya ce dan nata wanda ake zargin yana sana’ar muggan kwayoyi kuma ya dade yana rigima da ita kan halinsa, ya zabi ya kashe ta.

Sai dai, Mista Ben Obi, shugaban al’umma a Inyi, wanda ya zanta da ‘yan jarida da dama, ya nuna cewa matsalolin sun fara ne makonnin da suka gabata lokacin da wanda ake zargin ya samu sabani da kanin wanda ake zargin.

DSP Daniel Ndukwe, kakakin rundunar ‘yan sandan, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce an kama wanda ake zargin kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Ndukwe ya bayyana cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

“An kama wanda ake zargin, kuma ana kan bincike kan lamarin. Za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala bincike,” inji shi.

breaking news in nigeria today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp