Rundunar ƴan sanda a jihar Kano, ta tabbatar da gano gawar wata matashiya ƴar shekara 20 ɗauke da juna biyu yashe a gefen titi a ƙauyen Anadariya da ke ƙaramar hukumar Bebeji.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama mutum biyu da ake zargi da tafka aika-aikar.
Ya ce kamen ya faru ne sakamakon rahoton da mazauna yankin suka shigar lamarin da ya sa kwamishinan ƴan sandan jihar, Mamman Dauda ya tura jami’ansa zuwa inda lamarin ya faru.
Kakakin rundunar ya bayyana sunan matashiyar da Theresa Yakubu inda ya ce mutanen da ake zargi da kashe ta saurayinta ne da kuma abokinsa.
Saurayin marigayiyar ya amsa aikata laifin inda ya ce shi ya ƙunsa mata ciki kuma ya hada baki da abokinsa su kashe ta bayan da duk wani yunƙuri na zubar da jaririn cikin ya ci tura.
A nasa ɓangaren, kwamishinan ƴan sandan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayiyar inda kuma ya bai wa al’ummar yankin tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da adalci.
Ya kuma nemi mazauna unguwar su taimaka da bayanan da za su kai ga cafke sauran mutanen da ke da hannu a lamarin.