Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, ta kama wasu gungun ‘yan fashi da makami da suka kware wajen yiwa masu tuka babur fashi da makami.
An kama ’yan kungiyar ne a Neni da ke karamar hukumar Anaocha ta Jihar Anambra a lokacin da suke gudu da babur uku da suka sace daga wani ma’aikaci a Awka.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya raba a Awka.
Ikenga ya ce: “’Yan sanda a Neni sun damke wasu ’yan fashi da makami da suka yi awon gaba da wata mota kirar Tricycle a Agu-Awka a ranar 15/7/2023 (daren Asabar).
“An ragargaza ’yan kungiyar ne biyo bayan bayanan da aka samu daga ‘yan sanda a Awka cewa ‘yan kungiyar na guduwa zuwa karamar hukumar Anaocha.”
Kakakin, wanda ya bayar da bayanin kamun ya ce: “’Yan sandan da ke sintiri tare da ‘yan banga na yankin sun yi wa ‘yan fashin kwanton bauna, inda suka samu nasarar cafke su.
“An kwato bindigar Baretta daya da wani babban bindiga mai suna Chief Revolver Pistol, harsashi guda goma sha biyu, da alburusai guda daya da aka kashe daga barayin mutane uku. An kuma gano Tricycle. ”
Ya lissafo wadanda ake zargin sun hada da: Ebuka Madu mai shekaru 22 dan Umunze, Chinedu Godwin mai shekaru 23 daga jihar Enugu da Udegbunam Chikezie mai shekaru 18 a Neni.
Ikenga ya ruwaito kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aderemi Adeoye yana tabbatar wa da jama’a cewa amincewar da aka baiwa rundunar don tabbatar da doka da oda, da bin adalci ba za a yi wasa da su ba.
Ya kara da cewa, “Ya bayar da umarnin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan gudanar da bincike mai zurfi.”


