Rundunar ƴan sandan Abuja ta kama wasu gawurtattun masu garkuwa biyar a yankunan Gwagwa da Dei-Dei bayan samamen da jami’an rundunar suka kai kan maɓoyar su tsawon yini biyu.
Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce jami’an rundunar sun kai samamen tsakanin 30 ga watan Yuni da kuma 3 ga watan Yuli bayan samun bayanan sirri.
Mutanen da aka kama su biyar da shekarunsu tsakanin 20 zuwa 29, ana zarginsu da hannu da sace wasu mutane a Gwagwa ranar 12 ga watan Yuni inda suka karɓi kuɗin fansa naira miliyan 12 daga wajen iyalansu inda kuma suka kashe mutum biyu.
Ana kuma zargin mutanen da aka kama da sace-sacen mutane da aikata miyagun laifuka a sassan babban birnin Najeriyar.
Rundunar ta ce an ƙwace bindiga huɗu ƙirar AK47 da alburusai a hannun mutanen bayan da suka tabbatar da miyagun ayyukan da suka aikatawa.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen, kwamishinan ƴan sandan Abuja, Benneth Igweh ya nanata ƙudirin rundunar na tabbatar da tsaron al’ummar birnin.