Rundunar ƴansanda a babban birnin Najeriya, Abuja ta ce, ta kai farmaki kan wata moɓoyar wasu mutane da ake zargi da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa a birnin.
Ƴansandan sun ce sun kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri, abin da ya sa suka yi wa ƴanbindigar kwanton ɓauna a sansanoninsu a dajin Kwati da ke yankin jihar Kaduna.
Inda suka yi nasarar kama hudu daga cikin waɗanda ake zargin, sannan suka kuɓutar da wasu mutanen da ake garkuwa da su.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan ta Abuja, Josephine Adeh ta ce sun kai samamen ne tare da taimakon jami’an DSS da sojoji da kuma ƴanfarauta.
Ta kuma ƙara da cewa sun kama bindigogi a lokacin samamen.
Matsalar satar mutane domin karɓar kuɗin fansa ta fara yawaita a Abuja, inda a baya-bayan nan aka kama wasu ƴangida ɗaya a yankin Bwari, inda har ta kai ga kashe ɗaya daga cikinsu.