An kama manajan wani jirgin ruwan da ya kife ranar Litinin a jihar Legas, bisa zarginsa da yin sakaci da rashin bin ka’idojin tsaro.
Shugabar hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa a yankin Legas, NIWA, Misis Sarat Braimah, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Legas.
Ta ce an kama shi ne sakamakon wani bincike da aka yi dalla dalla kan lamarin.
“An kama shi ne da nufin tabbatar da bin diddigi da kuma kafa misali mai tsauri na bin ka’idojin hanyoyin ruwa don hana afkuwar lamarin nan gaba. Ana ci gaba da gudanar da wasu matakai na shari’a yayin da ake ci gaba da bincike,” inji ta.
A cewarta, dole ne ma’aikacin jirgin ya fito da kyaftin din jirgin, yana mai jaddada cewa, an tabbatar da cewa jirgin ruwan fiber ya kauce daga tasharsa, ya kuma yi karo da wani jirgin ruwan katako saboda cikas da kyaftin din.
Braimah ya ce wannan cikas ya samo asali ne saboda lodin da ke cikin jirgin ruwan fiber, yana mai cewa jirgin mallakar Only God Ferry ya gaza bin ka’idojin tsaro da kuma hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa.


