Rundunar ƴan sandan Najeriya ta fara gudanar da bincike a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar, bayan da ta ɗamke wani malamin allo bisa zargin kashe ɗaya daga cikin almajiransa, kuma ya cire masa wasu sassa na jiki.
Malamin allon dai yana samar da bayanai masu muhimmanci ga faɗaɗa bincike da rundunar ƴan sandan take yi.
Yanzu haka an fara gano bakin zaren zargin aikata wannan kisa, kamar yadda SP Lawan Shi’isu Adam, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Jigawa ya bayyana wa BBC.