Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta cafke wasu dalibai hudu na jami’ar jihar Kwara, KWASU bisa zargin su da lakada wa ‘yan uwansu duka har lahira.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Toun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar wa manema labarai kamun ranar Juma’a a Ilorin.
A cewarsa, ana ci gaba da gudanar da bincike kan zargin kisan.
Rahotanni na cewa wasu daliban KWASU sun lakada wa ‘yan uwansu duka har lahira saboda sun dauki hoton bidiyo.
Lamarin dai ya faru ne a wani dakin kwanan dalibai masu zaman kansu da ke wajen harabar makarantar.