Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun kama wani da ake zargin dan fashi ne da ya yi awon gaba da wata motar tirela dauke da tan 35 na man gyada wanda kudinsa ya kai kusan Naira miliyan 30.
Rundunar ‘yan sandan ta ce hedikwatar ‘yan sanda ta Toro ta samu kiran gaggawa game da satar motar da aka yi a tashar tirela ta Maraban Jos a jihar Kaduna a ranar 12 ga Afrilu, 2024.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya ce motar da aka sace, kirar DAF CF 85, ta fito ne daga Umuahia da ke Jihar Abia, ta nufi Jihar Kano a lokacin da aka sace ta a Jihar Kaduna.
Sanarwar ta ce, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa direban motar ya tsaya a kusa da tashar tirela ta Maraban Jos domin yin wanka sai daga baya ya dawo ya gano cewa tirelar ta bace daga inda aka ajiye ta.
Sanarwar ta kuma kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Auwal Muhammad, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na gaskiya da hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (SCID) kan satar motar.
Rundunar ‘yan sandan ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike kan lamarin.