Rundunar tsaro ta Amotekun a jihar Osun, ta kama wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne da kuma dan fashi.
An kama mutanen biyu daban-daban a Ila-Orangun da Osogbo ranar Alhamis.
Kwamandan rundunar, Birgediya Janar Bashir Adewinmbi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce, “An kama Sodiq Adelabu mai shekaru 20, dan asalin Osogbo ne a Osogbo bisa zarginsa da kasancewa dan kungiyar asiri, yana aikata ayyukan asiri da kuma sata.
“Wanda ake zargin ya amince cewa shi mamba ne na kungiyar Eiye Confraternity lokacin da ake masa tambayoyi.
“Wanda ake zargi na biyu, Sunday Oluwasegun, mai shekaru 22, dan asalin Ila-Orangun, an kama shi ne da laifin shiga gida da sata a Garin Ila-Orangun.
“An ba da rahoton cewa ya sace wasu kudi da wasu kayan aikin gida kafin daga bisani a kama shi.”
A cewar Adewinmbi, an kama su ne bayan da mazauna yankin suka shigar da kara a kansu da kuma ayyukansu.