fidelitybank

An cafke ƴan sanda biyu da suka ci zarafin wani mutum

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, ta cafke wasu jami’anta guda biyu da ke aiki a rundunar a kan wani faifan bidiyo da ke yaduwa a shafukan sada zumunta wanda ya kama su suna cin zarafin wani mutum mai suna Iyke a karamar hukumar Oyibo ta jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nwonyi Polycarp-Emeka, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi tir da harin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CP, Grace Iringe-Koko, ta bayyana haka, inda ta ce a halin yanzu jami’an da abin ya shafa suna gaban kotu bisa laifin rashin da’ar da suka aikata, matakin da ya ce zai kawo cikas ga sauran jami’an ‘yan sanda.

Sanarwar ta kuma yi kira ga wanda abin ya shafa da ya fito ga sashin hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, domin bayar da bayaninsa tare da taimaka masa wajen kammala binciken, tare da tabbatar da cewa za’a kare sunan sa.

Ta ce: “Kwamishanan ‘yan sanda, CP Nwonyi Polycarp Emeka, ya yi Allah wadai da cin zarafin da ‘yan sanda suka yi wa wani mutum a wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta.

“An gano ’yan sandan da ke cikin bidiyon kuma an kama su. A yanzu haka suna hannun rundunar ‘yan sanda ana shari’a kan rashin da’ar da suka aikata wanda zai zama hana wasu ‘yan sanda katsalandan.

“Kwamishanan ‘yan sandan ya tabbatar wa da jama’a cewa za a binciki jami’an ‘yan sanda bisa wasu ka’idojin da suka shafi dabi’ar ‘yan sanda da kuma sanya takunkumin da ya dace.

“Rundunar ta kara tabbatar wa mutanen jihar Ribas nagartaccen kudirin ta na inganta bin doka da oda.”

Mutumin da ya kama lamarin, ya bayyana matakin da ‘yan sandan suka yi da irin aikin da rundunar ‘yan sandan da ke yaki da ‘yan fashi da makami ta rusa.

Ya kara da cewa irin wannan aika-aikar da ‘yan sanda ke yi ya sha faruwa a Oyigbo.

dailysun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...
X whatsapp