Hukumomin da ke kula da daya daga cikin masallatai mafiya tsarki da muhimmanci da kuma tarihi a India, Jamaa Masjid a birnin Delhi, sun janye dokar da suka sanya ta hana duk wata mata da ba ta tare da muharraminta shiga masallacin.
A baya sun sanya dokar ne da cewa yawancin masu ziyarar masallacin suna saɓa martabar wurin.
To amma yanzu sun janye dokar bayan da wani jami’in gwamnati ya bukaci hakan.
Tun da farko wani mai magana da yawun hukumar masallacin ya ce wasu matan da ke zuwa suna fakewa da ziyarar ne, inda suke haduwa da samarinsu, ko kuma su dauki hotunan bidiyo da suke sanyawa a shafukan sada zumunta da muhawara.