fidelitybank

An bude karbar sakamakon zabe na kasa

Date:

Shugaban Hukumar Zaɓe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ayyana buɗe zauren karɓar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a hukumance.

Shugaban na INEC ya ce za a fara tattara sakamakon ne daga gundumomi zuwa ƙananan hukumomi, daga nan sai a kai matakin jiha.

Ya ce bayan nan ne kuma za a kai sakamakon zuwa Abuja, babban birnin tarayya, a zauren tattara sakamakon.

Yakubu ya ce baturen zaɓe idan ya zo sanar da sakamakon zaɓen jihar da ya zo da ita, zai faɗi ta yadda kowa zai ji, inda zai faɗi yawan mutanen da aka yi wa rajista da waɗanda suka samu damar kaɗa kuri’a da kuma kuri’un da suka ɓaci.

Karanta Wannan: Da Dumi-Dumi: An kona ofishin INEC na Takai a Kano

Shugaban na INEC ya ce bayan haka baturen tattara sakamakon zaɓen kowace jiha zai faɗi yawan kuri’un da kowace jam’iyya ta samu, sannan sai a kira wakilan jam’iyya su zo su sanya hannu idan suka amince da sakamakon.

Shugaban na INEC ya yi kira ga dukkan wakilan jam’iyyu da kuma ‘yan jarida da su tabbatar da cewa sakamakon zaɓen da hukumar ta sanar kaɗai za su yaɗa.

Ya ƙara da cewa babu wani wuri da ake sanar da sakamakon zaɓen illa babban zauren da aka tanada.

Yanzu dai an tafi hutun har zuwa karfe shida na yamma lokacin da za a dawo domin fara sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar gadan-gadan.

legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp