An bude taron kasashe masu tasowa da aka yi wa lakabi da G-77 a birnin Havana na kasar Cuba.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ne ya bude taron na kwanaki biyu.
Shugabannin kasashen Afirka fiye da 30 da na yankin Latin da Asiya ne ke halartar taron.
A jawabinsa na bude taron Mista Gutteres ya ce duniya ta gaza a kan kasashe masu tasowa, ya kuma jinjina wa kungiyar bisa kokarinta na tallafa wa mambobinta,
Gutteres ya kara jadda muhimmancin hada karfi waje guda domin magance matsalar sauyin yanayi.
G-77 dai babbar kungiya ce a Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke kunshe da mambobi 134.
Duk da kasancewarta ba mambar kungiyar ba, kasar China na halartar taron na wannan shekara.


