An binne tsohon shugaban Iran Ebrahim Raisi a birnin Mashhad, na biyu mafi girma a ƙasar kuma mahaifarsa.
Raisi ya rasu ne ranar Lahadi sanadiyyar hatsarin jirgin sama, tare da ministan harkokin waje na ƙasar da kuma wasu mutanen shidda.
Dubban mutane ne suka kwarara a kan titunan birnin na Mashhad domin nuna alhini da rasuwar tasa.
Sun riƙa jefa furanni kan motar da ke ɗauke da gawarsa yayin da rake kan hanyar maƙabartar Imam Reza, wuri mai matuƙar tsarki a Iran.
Yanzu hankali zai koma kan wanda zai gaji Raisi, wanda kafin rasuwarsa aka yi zaton cewa shi ne zai gaji jagoran musulunci na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.