An binne Oba Adeyemi a tsohon garin Oyo ranar Asabar.
Adeyemi ya mutu ne a ranar Juma’a, a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola, Ado Ekiti.
Tuni dai aka kai gawar Alaafin na Oyo fadar sa.
Tun da farko, Yusuf Ayoola, shugaban kungiyar Oyomesi, ya bayyana cewa za a yi jana’izar marigayi Alaafin a yau.
Ya ce an yi abubuwan da suka dace.