An gudanar da jana’izar mutanen da suka mutu sakamakon fashewar wata tankar mai a jihar Jigawa.
Gwamna Umar Namadi da manyan jami’an gwamnati ne suka jagoranci jana’izar a garin Majiya na ƙaramar huukumar Taura, inda hatsarin ya faru.
Zuwa yanzu dai hukumomi sun ce waɗanda suka mutu sun kai 104, yayin da sama da 100 kuma suka jikkata.
Shaidu sun shaida wa BBC cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami’an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.