An binne gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura na jihar Katsina da misalin karfe 5:50 na yamma.
A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli ne Muhammadu Buhari ya rasu a birnin Landan na Birtaniya bayan shafe dogon lokaci yana jinya.
Muhammadu Buhari ya rasu ne yana da shekara 82 a duniya, shekara biyu bayan sauka daga muƙamin shugaban ƙasa.
Buhari ya mulki Najeriya a matsayin soja daga watan Disamban shekara ta 1983 zuwa watan Agustan 1985 kafin tuntsurar da gwamnatinsa.
Sai dai a shekara ta 2015 Buhari ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa bayan kayar da shugaba mai ci a wancan lokaci Goodluck Jonathan.
An rantsar da shi a matsayin shugaban farar hula, inda ya yi mulki Najeriya wa’adi biyu (shekara 8) daga ranar 29 ga watan Mayun 2025 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.
Sai dai Buhari ya yi ta fama da jinya tun farko-farkon mulkinsa na farar hula, inda ya riƙa safa da marwa daga Najeriya zuwa Landan domin neman lafiya.
Masharhanta na ganin cewa rashin lafiyar tasa ta rage karsashinsa a harkar shugabanci.
A ɓangare ɗaya kuma masu suka sun zargi gwamnatinsa da ɓoye rashin lafiyar da ke damun sa.
Muhammadu Buhari ya rasu ya bar mata É—aya – A’isha Buhari – da Æ´aÆ´a 10.