fidelitybank

An bindige jami’an Road Safety 2 a Anambra

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun kai wa tawagar jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC hari da suka hada da wani jami’i, direba, da wasu ma’aikata biyu a jihar Anambra.

A yayin harin da aka kai ranar Lahadi a kan hanyar Igbo-Uku-Uga a jihar, maharan sun kashe mutane biyu tare da jikkata daya.

Rundunar dai na gudanar da aikin sintiri na yau da kullum a yankin ne ‘yan bindigar suka bude musu wuta, inda suka kashe jami’an, gawar guda biyu yayin da daya kuma ya tsere cikin daji.

An garzaya da shugaban tawagar wanda ya samu munanan raunuka zuwa asibiti.

A nasa martani, Shugaban Rundunar, Dakta Boboye Oyeyemi, ya yi tir da harin tare da jajantawa iyalan ma’aikatan da suka mutu.

Ya kuma jajantawa kwamandan runduna da ma’aikatan rundunar FRSC ta Igbo-Uku, da ma daukacin jami’an hukumar da ma’aikatan hukumar bisa wannan rashi.

Oyeyemi ya tabbatar musu da cewa tuni rundunar ta fara aiki tare da rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro da abin ya shafa, domin ganin an kama wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da basu damar fuskantar cikakken tsarin doka.

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp