Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa Mista Safiyanu Andaha.
An sace Mista Safiyanu ne tare da wani Alhaji Adamu Custom.
Maharan sun yi awon gaba da mutanen ne a ranar Litinin da misalin karfe 8:30 na dare a lokacin da suke murnar sabuwar shekara.
Mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Nasarawa kan harkokin kananan hukumomi da masarautu, Mista Haruna Kassimu ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, jami’an tsaro sun mayar da martani cikin gaggawa, amma ‘yan bindigar da karfi sun gudu tare da shugaban karamar hukumar zuwa inda ba a san inda suke ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin a daren ranar Litinin.
Ya ce rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro na kan bin diddigin masu garkuwa da mutane domin ganin an sako mutanen.