Jami’an tsaro na ci gaba da ran gadi a birnin Benin gabanin zaɓen gwamnan jihar Edo. Shugaban Tawagar Yansanda da za su yi aikin zaɓen, DIG Frank Mbah ya ce za su yi wa kowa adalci.
BBC ta shaida cewa jama’ar birnin na ci gaba da hada-hada kuma da yawansu sun shaida cewa za su fita domin kaɗa kuri’a, sai dai wasu mutanen sun ce tsoron rikici zai iya hana su fita yin zaɓen.
A gobe Asabar ne dai za a gudanar da wannan zaɓe.