Rundunar ‘yan sanda, ta bayar da belin Hudu Yunusa-Ari, kwamishinan zabe na jihar Adamawa (REC) da aka dakatar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Muyiwa Adejobi ya tabbatar da belin a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Yunusa-Ari dai ya kasance a gidan yari domin yi masa tambayoyi bisa zarginsa da aikata ba daidai ba a lokacin zaben gwamnan jihar Adamawa da aka kammala.
“Ana sa ran zai kai rahoto a hedikwatar ‘yan sanda a duk ranar mako yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin,” Adejobi ya kara da cewa.
Yunusa-Ari ya sanar da Aisha Binani ‘yar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce ta lashe zaben da aka yi a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata.