Shugaban Jam’iyyar Maharashtra Navnirman Sena (MNS) Raj Thackeray ya ce ba ya son tashin hankali a Maharashtra. Don haka ya ce Musulmi su fahimci babu addinin da ya fi ƙarfin doka.
Ya ce buƙatarsa ta cire lasifika daga Masallatai ba ya nuna adawarsa ba ne ga Sallar da Musulmi suke yi, kuma haka jam’iyyarsa ba ta son tashin hankali.
An ba Musulmi wa’adi su cire lasifika a Masallatai a Maharashtra zuwa ranar 2 ga watan Mayu. “Zuwa 3 ga Mayu za a ga abin ya kamata a yi.”
“Idan har ba a cire Lasifika a Masallatai ba zuwa 3 ga Mayu, to ma’aikatan MNS za su yi amfani da lasifika suna rera Hanuman Chalisa a Masallatan.
Rikicin addini a Indiya tsakanin Musulmi da Hindu na ƙara ƙamari, lamarin ya munana a cikin ‘yan shekarun nan, sakamakon yadda ‘yan Indiya ke jifan juna da kalaman kiyayya.