A ranar Talata ne babban sifeton ‘yan sandan, IGP Usman Baba, ya umarci kwamishinan ‘yan sandan da ke aikin zabe a jihar Adamawa, Mohammed Barde, da ya janye daga jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, ya ce umarnin ya fara aiki nan take.
Adejobi ya ce IGP din ya kuma umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe, CP Etim Equa da ya gaggauta zuwa jihar Adamawa domin tabbatar da tsaro a zaben gwamnan da ba a kammala ba.
Ya ce, “IGP ya bayar da umarnin cewa kwamishinan ‘yan sanda kan harkokin tsaro a jihar Adamawa, CP Barde ya janye daga jihar Adamawa, shi kuma kwamishinan ‘yan sanda mai kula da jihar Gombe, CP Etim Equa ya garzaya Adamawa cikin gaggawa, domin ku je ku sa ido kan zaben da bayar da bayanan da suka dace da kuma tabbatar da cewa tsarin ya yi nasara.”
A halin da ake ciki, an tsaurara matakan tsaro a cibiyar tattara sakamakon zaben jihar Adamawa yayin da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke ci gaba da zama kwanaki bayan da hukumar ta dakatar da atisayen.