Majalisar ƙasar Chadi ta ɗaga darajar shugaban ƙasar, Janar Mahamat Deby zuwa muƙamin Field Marshal, wanda shi ne muƙami mafi girma a rundunar sojin ƙasar.
Ƴanmajalisar sun ɗauki wannan matakin ne bayan kaɗa ƙuri’a a ranar Litinin, inda suka ce, “an ɗaga muƙaminsa saboda sadaukawarsa ga ƙasar da ma rundunar soji, da kuma nasarorin da sojoji ke samu a ciki da wajen ƙasar.”
Ƴanmajalisa 160 ne suka kaɗa ƙuri’ar amincewa, biyu suka ƙi amincewa, sannan shida ba su halarci zaman ba.
An daga muƙamin Mahamat Deby ne a bayan ya ƙaddamar da yaƙi da Boko Haram a yankin tafkin Chadi, bayan wani hari da suka kai ga sojojin ƙasar.
An ruwaito cewa shi ne ya jagoranci sojoji zuwa fatattakar ƴan Boko Haram, wanda aka yi mako biyu ana gwabzawa.
Ya karɓi mulki ne daga mahaifinsa Idris Deby Itno, wanda shi ma ya samu muƙamin a shekarar 2020 yana mai shekara 68.
A watan Mayu ne aka zaɓi Mahamat a matsayin shugaban ƙasar Chadi, inda ake tunanin zai bi tafarkin mahaifinsa wajen yin mulki ba sani ba sabo.