Kwale-kwalen da ya ta tashi daga ƙauyen Gwajibo Mudi, a hukumar Kaiama ta jihar Kwara da ƙarfin aƙalla 300 da ke kan hanyarsu ta zuwa maulidi a garin Gwajibo na jihar Niger.
Jirgin ya kife ne da fiye da 150 galibinsu mata da yara, lamarin da ya jefa al’ummar yankin da dama cikin hali da damuwa.
Tuni dai shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya aike da saƙon ta’aziyya ga nuna lamarin ya rutsa da su, tare da bayar da gudummawar domin gano musabbain hatsarin.
Tinubu ya kuma bayar da umarni ga jami’ai su tabbatar masu tuƙa kwale-kwalen ba su saɓa dokar tuƙu ba.