Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, National Emergency Management Agency (Nema), ta ce an kwaso ƙarin ‘yan ƙasar 99 da suka maƙale a Jamhuriyar Nijar.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin ƙarfe 2:15 na ranar yau Litinin bayan ƙungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta ƙasashen duniya IOM ta ɗebo su.
Sai dai Nema ba ta yi ƙarin bayani kan abin da ya maƙalar da su ba. Amma ‘yan Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma kan yi sansani a Nijar a yunƙurinsu na tsallakawa Turai ta ɓarauniyar hanya.
Cikin mutanen akwai maza manya 76, da mata manya 15, da yara mata bakwai, da yara maza 15, da jaririya ɗaya.