Ƙasar Amurka za ta bayar da ƙarin tallafin dala miliyan biyar, domin taimaka wa yankunan da ambaliya ruwa ta shafa a faɗin ƙasar nan.
Tallafin ƙari ne kan dala miliyan ɗaya da hukumar bayar da tallafi ta ƙasar Amurka ta bayar domin taimaka wa waɗanda ambaliya ruwa ta shafa a ƙasar.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya sauka a daminar bana ya shafi fiye da mutum miliyan 4.4 a faɗin ƙasar, lamarin da ya raba mutum akalla miliyan 2.4 da muhallansu, tare da lalata dubban gidaje. Inda kuma sama da mutum 660 suka rasa rayukansu.